✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta kashe ’yan gudun hijira 14 a Borno

An tabbatar da rasuwar ’yan gudun hijira mutum 14 yayin da wasu mutum 15 suka samu mummunan rauni lokacin da wata gobara ta tashi a…

An tabbatar da rasuwar ’yan gudun hijira mutum 14 yayin da wasu mutum 15 suka samu mummunan rauni lokacin da wata gobara ta tashi a wani sansanin ’yan gudun hijira da ke karamar Hukumar Ngala a jihar Borno.

Gobarar dai ta tashi ne da misalin karfe 2:15 na rana a ranar Alhamis a sansanin ’yan gudun hijira da ke Ngala IS.

Rahotanni na bayyana cewa, an yi nasarar kashe gobarar da ta tashi.

Akalla wutar ta raunata kimanin mutum 1250, yayin da aka tabbatar da cewa, mutum 14 sun mutu, 15 sun samu mummunan rauni.

Hukumomi na ci gaba da binciken dalilin tashin gobarar don daukar mataki na gaba.

Sansanin ‘yan gudun hijira da ke Karamar Hukumar Ngala lokaci da gobara ta tashi