✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kone gawarwaki sama da 400 a asibitin Anambra

Gobarar ta tashi ne a sashen adana gawarwakin asibitin Onitsha.

Sama da gawarwaki 400 ne suka kone kurmus sakamakon wata gobara da ta tashi a sashen adana gawarwaki na babban asibitin Onitsha da ke Jihar Anambra.

A cewar daya daga cikin masu kula da gawarwaki a asibitin wanda ba ya so ambaci sunansa, ya ce yana zargin fatalwoyi ne suka tayar da wutar.

Ya ce, “Ko ana jajiberin ranar da lamarin zai faru, mun fito aiki muka tarar an fito da gawarwaki sama da 10. Ba mu san wanda ya yi hakan ba.

“Tsawon shekarun da na kwashe ina wannan aikin, na gano cewa gawarwaki sukan yi fushi kamar yadda masu rai ke yi. Mu kan ji hakan kullum da daddare.

“Na yi amanna sune suka ta da wannan gobarar saboda watakila sun fusata, amma in ban da haka, babu abin da zai sa wuta ta tashi a nan ba tare da sa hannun mamatan ba.

“Wasu daga cikinsu da suka dade a nan iyalansu ba su zo sun dauke su ba suna yin abubuwan ban mamaki sosai,” inji majiyar.

Aminiya ta gano cewa gobarar wacce ta shafe kusan sa’o’i uku tana ci ranar Asabar, ta kone sashen adana gawarwakin da ke cikin asibitin.

Rahotanni sun ce ta samo asali ne daga wani daji da ke bayan asibitin, wanda ya kama da wuta.

Ma’aikatan sashen dai sun yi ta kokarin kashe gobarar amma ta fi karfinsu, sai da suka kira ’yan kwana-kwana.

To sai dai a cewar Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Mista Martin Agbili, wutar ta samo asali ne daga dajin da ke bayan asibitin.

“Mun gano cewa gobarar ta samo asali ne daga dajin da ke bayan asibitin, shi yasa muka jima muna shawartar jama’a da su rika nome muhallansu, musamman a lokacin sanyi, saboda in wuta ta taso babu abin da zai tare ta,” inji shi.

Ya ce ko da yake ba a samu asarar rayuka ba, amma ma’aikatan da suka yi yunkurin kasheta sun samu raunuka, yayin da su kuma gawarwakin suka kokkone.