✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta kone gidaje 40 a Fatakwal 

Ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar tukunyar gas din girki.

Gobara ta kone wasu gine-gine a biyu da ke dauke da gidaje akalla 40 a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

Gobarar ta tashi ne a kewayen titin Boms da ke unguwar Elekahia da misalin karfe 11 na safe.

An ruwaito cewa ta kone gidaje biyu, daya mai da gidajen bulo, dayan kuma gine-ginen katako, cikin kasa da awa daya.

An ce gobarar ta tashi ne daga daya daga cikin dakunan da ke rukunin gidajen da wata mata ke dauke da su kuma ana kyautata zaton gobarar ta tashi ne a dalilin fashewar tukunyar gas.

Aminiya ta gano yadda wutar ta yi barnar mai yawan gaske lamarin da ya sanya motocin kashe gobara wuyar kashewa.

Hukumomi a jihar ba su tantance kimar barnar da gobarar ta yi ba da kuma musabbabin tashin gobarar ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.