✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta kone rumfuna 63 a kasuwar Zamfara

Ana zargin wutar ta samo asali ne daga wani shagon sayar da danyen kifi.

Wata gobara da ta tashi ranar Lahadi a kasuwar Tudun Wada dake Gusau babban birnin jihar Zamfara ta yi sanadiyyar konewar shaguna 63 kurmus.

Rahotanni sun ce ana zargin wutar ta samo asali ne daga wani shagon sayar da danyen kifi bayan da aka sami tangardar wutar lantarki a cikinsa.

Yayin da ya ziyarci kasuwar, Gwamnan jihar ta Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya jajantawa ’yan kasuwar da suka tafka asarar inda ya shawarce su da su dauke ta a matsayin wata kaddara daga Allah.

Ya kuma shawarci ’yan kasuwar da su tabbata suna kashe dukkan kayayyakin wutar lantarki a shagunansu kafin su rufe su bayan gama cinikinsu a kullum.

Gwamna Matawalle ya kuma ce gwamnati za ta sake gina shagunan da suka kone, tare da umartar Kantoman Karamar Hukumar Gusau da ya fara aikin ba tare da bata lokaci ba.

Kazalika, Gwamnan ya kuma kafa wani kwamiti karkashin fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar, Sheikh Ahmad Umar Kanoma domin tantance irin asarar da ’yan kasuwar suka tafka a gobarar sannan ya mika rahotonsa cikin kwanaki bakwai ga gwamnatin jihar domin ta taimaka musu su dawo harkokinsu kamar yadda ya kamata.

Gwamnan ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da taimakawa ’yan kasuwa da ma harkokin kasuwanci domin ganin jihar ta ci gaba.