✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kone shaguna 42 a jami’ar ATBU da ke Bauchi

Gobarar ta tashi ne da tsakar dare lokacin shagunan na kulle

Wata gobara ta tashi da tsakar dare a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi, inda ta kone shaguna 42.

Rahotanni sun ce gobarar dai ta janyo asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira.

Shagunan da suka kone sun hada da cibiyoyin kasuwanci na na’ura mai kwakwalwa da shagon gyaran gashi na mata da kuma shagunan sayar da kayayyaki.

Ana zargin gobarar ta tashi ne wajen karfe 2:00 na tsakar daren Laraba, kuma ta yi da barna ne saboda lalacewar motar kashe gobara ta jami’ar.

Wani ma’aikacu a jami’ar ya ce: “Na samu labarin cewa a lokacin da gobarar ta tashi sun sanar da jami’an kashe gobara na jami’ar amma sun ce batirin motar ta lalace, sun ce sun kai rahoto ga jami’an hukumar su saki kudi domin a gyara ko kuma a gyara ta ga wata sabuwa a sayo, amma ba a yi komai ba.

“Sun ce sun ci gaba da rubuta wa hukumar kula da kudaden da suka sayo don sayen sabuwar batir, amma wai sun ce babu kudi,” inji shi.

Shi ma wani da shagonsa ya kone, Yarima Hosea Mathias, ya ce ya samu waya da misalin karfe 4:00 na safiyar Alhamis daga wani wanda ya shaida masa cewa shagunansu na cin wuta.

Ya ce an sanar da shi cewa wutar lantarki ce ta haddasa gobarar.

Mathias ya kara da cewa, “Ina gudanar da kasuwanci ta kwamfuta da hanyoyin sadarwa na IT, na rasa duk wani abu da nake da shi a cikin shagona, kwamfutoci, kayan daki, janareta, injina, injinan POS da abubuwa da dama.”

Shi kuwa wani mai shagon, Alfred Joseph, ya ce ko tsinke bai samu daula daga shagon nasa ba.

Ya ce wani abokinsa ne ya kira shi ya shaida masa cewa shagonsa ya kone gaba daya.