✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kone shaguna da gidaje sama da 300 a kasuwar kayan gine-gine a Legas

Gobarar ta tashi ne lokacin da ’yan kasuwa ke kokarin rufe shagunansu ranar Juma’a.

Kadarori na miliyoyin Nairori ne gobara ta kone a kasuwar sayar da kayan gine-gine ta Oke-Afa da ke Ejigbo a Jihar Legas.

Lamarin, wanda ya faru da daren Juma’a dai ya shafi akalla shaguna 300 da kuma gidaje biyu.

Gobarar dai ta fara ne wajen misalin karfe 9:30 na dare a kasuwar.

Kazalika, gobarar ta kone wani masallacin kasuwar da wata katangar wani wajen biki da kuma wasu manyan tankunan ruwa guda uku.

Tuni dai aka ankarar da jami’an bayar da agajin gaggawa da suka hada da na Jihar Legas (LASEMA), amma wutar ta ci gaba da ci har zuwa kashegarin ranar Asabar.

Shugaban hukumar ta LASEMA, Dokta Olufemi Oke-Osanyintolu, ya ce ba a samu asarar rai ko daya ba a gobarar, inda ya ce ta tura jami’an hukumar zuwa wajen.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton ya ce ba a kai ga gano musabbabin gobarar ba.

Ya yi kira ga ’yan kasuwar da su tabbata sun yi wa kayayyakinsu inshora, tare da tabbatar da suna kula da su, musamman ma a lokacin hunturu da aka fi barazanar tashin gobarar.

Wasu daga cikin ’yan kasuwar da suka zanta da wakilinmu sun ce gobarar ta tashi ne lokacin da suke kokarin rufe shagunansu ranar Juma’a.