✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta lashe Unguwanni takwas a Borno

Gidaje da dama sun kone a yayin wata gobara da ta tashi a garin Gajiganna da ke Karamar Hukumar Magumeri a Jihar Borno. Wutar wadda…

Gidaje da dama sun kone a yayin wata gobara da ta tashi a garin Gajiganna da ke Karamar Hukumar Magumeri a Jihar Borno.

Wutar wadda ta fara ci da misalin karfe 2.00 na rana a wannan lokaci na zafi, ta ta’azzara a sakamakon iskar bazara da ke kadawa.

Wani mazaunin garin mai suna Baa Kaka Ibrahim wanda ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho, ya ce wutar ta fara ci ne a rufin wani gida jin kadan bayan dawowar mai gidan.

A cewarsa, kasancewar rufin sauran gidajen da ke makwabtaka an yi su ne da kirare da kuma ciyayi gami da iskar bazara da ke kadawa, ya sanya wutar ta rika yaduwa cikin gaggawa wadda ta ci karfin mazauna yankin da suka rika kai komon kashe ta da ruwa da kasa.

Ya ce, gidaje gami da shaguna da kadarori da dama sun kone a yayin da gobarar ta rika yaduwa a garin da ke Arewacin jihar Borno.

Sauran yankunan da gobarar ta shafa sun hada da Gamboiri, Kangiri, Umara Misulali, Baare, Granbori, Tunjiram da kuma Swindi.

A watan da ya gabata ne makamanciyar wannan musiba ta gobara ta auku a wata zamantakewa ta ’yan gudun hijira da ke Maiduguri, babban birnin jihar.