✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta sake tashi a tashar jirgin ruwan Lebanon

Kwana 35 da fashewar ammonium nitrate a tashar jirgin ruwan ta kashe mutum fiye da 200

Gobara ta sake ta shi a tashar jiragen ruwan kasar Lebanon da a watan Agusta aka samu fashewar sunadarin ammonium nitrate da ya hallaka mutum 200 ya lalata fiye da birnin Beirut.

Bakin hayakin gobarar ya mamaye sararin samaniyar birnin Beirut sakamakon tashin wutar na ranar Alhamis, yayin da motocin daukar marasa lafiya ke kai-komo a wurin, jami’an kashe gobara ke kokarin kashewa wutar.

“Mun bude dukkanin tagogi, zanzu haka muna rumfar gidanmune. Har yanzu ina jin kasa na motsi. Yana tuna min abin da ya faru kwanankin baya,” a cewar Dana Awad, wata mata da ke zaune a Beirut.

Kamfanin dillancin alabaru na AP, ya ruwaito Rundunar Sojin kasar Lebanon ta ce wutar ta tashi ne a wata ma’ajiyar mai da ta’ayoyi, kuma ana kokarin kashe wutar.

A ranar 4 ga Agusta, 2020 ne kusan ton 3,000 na sinadarin ammonium nitrate da ke ajiye a tashar jirgin ruwan na birnin Beirut ya yi bindiga tare da haifar da asabar sama da Daliya biyan biyar a kasar da ke fama da rikicin siyasa.

Rushewar gine-gine da sauran kadarori da abin iftila’in ya haifar ta kai ga sai da kasashen duniya suka taimaka mata da kayan agaji domin jinya da samar da matsuguni ga wadanda abin ya shafa.

Kazalika gwamnatin kasar ta sallami dukkannin jami’anta dake da hannu a ginawa da kuma kula da ma’adanar ta kuma umarci sojoji su tsare su.