✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta tashi a dandalin bikin fina-finai a Masar

Wutar ta tashi kimanin awa 24 kafin fara shagalin bikin.

Gobara ta tashi a dandalin taron bude baje kolin fina-fanai na kasar Masar, lamarin ya sa aka nemi soke bikin.

Wutar ta tashi ne kasa da awa 24 kafin fara taron bude bikin, da aka shirya baje kolin fina-finan 80 na kasashen Larabawa da kasashen duniya.

Daya daga cikin wadanda suka shiriya bikin, Ola El-Shafei ya ce, “Har yanzu muna cikin zullumi, amma mun gode Allah da muka fito lafiya.”

Tashin wutar ta haifar da shakku game da fara bikin, amma an samu an kashe “Wutar da ta lalata wani bangare na babbar rumfar da aka shirya,” wata taron na El Gouna.

An garzaya zuwa asibiti mutum 15 da suka galabaita a sakamakon shakar numfashin da ta turnike bayan tashin gobarar, inji wani jami’in tsaro.

Taron fim din wanda attajirin Afirka, Samih Sawiris, ya karbi bakuncin taurarin masana’antar fim din Hollywood na kasar Amurka, ciki har da Forest Whitaker da Owen Wilson a shekarun baya.

“Zuwa gobe da dare komai zai kasance a shirye domin ci gaba da taron,” inji Sawiris a cikin wata sanarwa da ta ce matsalar wutar lantarki ne ta haddasa tashin gobarar.

Masu shirya taron sun kara da cewa za a gudanar da cikakken bincike kan abin da ya haddasa gobarar.

Karo na biyar ke na da za a yi bikin wanda za a kammala a ranar 22 ga watan Oktoban da muke ciki.