✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta tashi a Fadar Ooni na Ife

Rahotannin da Aminiya ta samu na cewa gobara ta tashi a Fadar Ooni na Ife a Jihar Osun, Oba Adeyeye Ogunwusi. Wutar da ba a…

Rahotannin da Aminiya ta samu na cewa gobara ta tashi a Fadar Ooni na Ife a Jihar Osun, Oba Adeyeye Ogunwusi.

Wutar da ba a kai ga kashe ta ba ta tashi ne a daya daga cikin gine-ginen da ke fadar basaraken.

Majiyarmu ta ruwaito Jami’in Gudanarwa da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Osun, Fatai Aremu, ya tabbatar da tashin gobarar.

Ya ce jami’an hukumar sun isa fadar Oba Adeyeye Ogunwusi domin kashe wutar da ta tashi.

Wasu rahotanni na cewa “wutar ba mai tsanani ba ce, sai dai mutane sun razana saboda kasancewar kofar shiga fadar a kulle”.