✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta tashi a gidan man AA Rano na Kano

Wani babur mai kafa uku ya kama da wuta sakamakon gobarar

Wata gobara da har yanzu ba a san musabbabin tashinta ba, ta dakatar da bada mai a gidan man AA Rano da ke titin Murtala Muhammad, daura da otel din Central da ke Kano.

Wani babur mai kafa uku dai ya kama da wuta sakamakon gobarar, amma an yi nasarar ceto mutanen da ke ciki bayan  an kashe wutar.

Wakilin Aminiya ya gano cewa akwai matatar Iskar Gas da ke makwabtaka da gidan man, kuma faruwar abin ke da waya tawagar ceto tay gaggawar janye motar gas din da ke harabar gurin.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai an fara gyaran gidan man, in da tuni masu fenti suka fara aikinsu.

Gidan man na AA Rano guda ne daga gidajen man da ke siyar da man fetir, da Iskar Gas, har ma Diesel a farashi mai rahusa a Kano.