✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta tashi a hedikwatar INEC da ke Enugu

Wutar ta kama a cikin dare, amma ba kai ga gano abin da ya haddasa ta ba.

Hediwatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), reshen Jihar Enugu ta kama da wuta a daren ranar Lahadi.

Ofishin ya kama da wuta ne mako guda bayan gobara a ofishin INEC na Karamar Hukumar Udenu ta Jihar.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Mohammed Aliyu, ya tabbatar ta tashin gobarar a ofishin da ke unguwar Achi, daura da Bankin Manoma, a Enugu.

Kwamishinan ’yan sandan ya ce yana wajen da gobarar ta shi don ba da dauki, amma bai amsa ragowar tambayoyin da aka masa ba.

Daga bisani an hangi Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, da ta Jihar Enugu na kai komo wajen ganin sun kashe wutar.

Kokarinmu na jin da bakin kakakin INEC na Jihar Enugu, Dokta Emeka Ononamadu, bai cimma nasara ba, domin bai amsa kiran wayar da aka masa a lokacin da wutar ke tsaka ci ba.