✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta tashi a hedikwatar ’yan sanda a Kano

Gobarar ta lakume wani babban rukuni a sashen gudanarwa na hedikwatar ’yan sandan.

Rahotanni da muka samu a yanzu sun tabbatar da cewa gobara ta tashi a hedikwatar ’yan sanda a Jihar Kano.

Wakilinmu da ya ruwaito labarin ya ce gobarar ta lakume wani babban rukuni a sashen gudanarwa na hedikwatar ’yan sandan ta Bompai da ke birnin Dabo.

Duk da cewa babu wani cikakken bayani ya zuwa hada wannan rahoto, mun samu cewa gobarar ta lakume muhimman wurare ciki har da na sashen kula da harkokin kudi, dakin taro, ofishin hulda da jama’a da sauransu.

Rahotanni sun ce gobarar ta cinye dukkan ofisoshin da ke saman benen ginin tun na shekarar 1967, in banda ofishin Kwamishina.

“Mun yi kokarin kashe gobarar ta hanyar amfani da na’urar kashe gobara ta hannu amma duk da haka wutar ta bazu zuwa wasu ofisoshin.

“Sai bayan an shafe kusan  sa’o’i 2 da tashin gobarar sannan ‘yan kwana-kwana suka isa wurin,” a cewar wata majiya.