✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta tashi a makarantar ma’aikatan BUK a Kano

Gobarar ta cinye ofishin shugaban makarantar da ofisoshin malamai

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce gobara ta kama tare da lalata wani sashe na Makarantar Firamaren Ma’aikatan Jami’ar Bayero ta Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya fitar a ranar Laraba a Kano.

Ya ce gobarar ta tashi a makarantar ce da yammacin ranar Talata.

A cewar Abdullahi, “Mun samu kiran waya da misalin karfe 05:53 na yamma daga wani Halliru Bello, inda nan take muka aike da tawagarmu zuwa wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 5:58 na yamma domin hana gobarar ta yadu zuwa wasu sassa na makarantar.

“Wani gini mai tsayi kafa 200 mai dauke da ofishin Shugaban Makarantar Firamaren da ofishin malamai maza da ofishin malamai mata da dakin ajiya da kuma bandaki sun kone a sanadin tashin gobarar.

“Ana binciken musabbabin tashin gobarar,” in ji shi.