✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta tashi a matatar mai ta Fatakwal

Wutar ta tashi ne daga jikin tankar, lokacin da take juye mai a cikin wani tanki.

Wata tankar mai mai cin lita 33,000 ta kone kurmus yayin wata gobara da ta tashi a matatar mai ta Fatakwal da ke Jihar Ribas ranar Asabar.

A cikin wata sanarwa da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya fitar da daren ranar Asabar, ya ce an samu nasarar kashe gobarar cikin kasa da sa’a biyu bayan tashinta.

Ya ce wata wuta ce ta tashi daga jikin tankar, lokacin da take juye mai a cikin wani tanki.

“Gobarar ta shafi tankar man ne kadai da kuma wajen da take juye man. Babu wata kadara ban da su da ta kone,” inji sanarwar.

NNPC ya kuma ce tuni hukumomin matatar karkashin jagorancin Shugabanta suka halarci wajen gobarar tare da taimakon Hukumar Kashe Gobara ta Kasa, inda suka kashe ta.

Hukumar matatar dai ta ba makwabtanta tabbacin cewa kada su tayar da hankulansu saboda gobarar

Aminiya ta rawaito cewa a watan Janairun 2021, Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu a wata yarjejeniya da kamfanin Tecnimont ta kusan Dalar Amurka biliyan daya da rabi don gyara ta.

NNPC ya ce yanzu haka aikin na ci gaba da gudana, kuma ana sa ran kammala shi nan da 2023.