✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kona ‘card reader’ 5,000′ a ofishin INEC

Wata daya kafin zaben gwamnan Ondo gobara ta kona ma'ajiyar na'urar zabe

Gobara ta tashi a ofishin Hukumar Zaben ta Kasa (INEC) reshen Jihar Ondo wata daya kafin zaben gwaman Jihar.

Da wuraren Isha’in ranar Alhamsin ne gobarar ta tashi ta kuma cinye na’uara tantance masu zaben (card reader) 5,141.

Kwamishinan INEC na Kasa kuma Shugaban Kwamitin Wayar da Kai na hukumar, Festus Okoye ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) hakan.

Okoye, wanda ke Akure domin shirye-shiryen zaben gwamnan jihar ta Ondon da za a gudanar a ranar 10 ga Oktoba, 2020, ya ce wutar ta tashi ne a dakin ajiyar na’urorin tantance masu zabe da misalin 7.30 na dare.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto, Okoye ya ce jami’an kwana-kwana na kokarin kashe gobarar.

Ba a kai ga bayyana musabbabin gobarar ba, amma Okoye ya ce abin da ya faru ba zai hana gudanar da zaben da ke tafe ba.

Ya ce duk da gobarar INEC za ta iya tattaro na’urorin zaben daga jihohin da ba a gudanar da zaben domin gudanar da na Ondo din.