✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta yi ajalin malami a Jigawa

Gobara ta yi ajalin wani matashin malamin Musulunci a Jihar Jigawa.

Gobara ta yi ajalin wani matashin malamin Musulunci mai shekara 29 a Jihar Jigawa.

Malamin mai suna Muhammad Ahmad, mazaunin kauyen Kuka ne da ke Karamar Hukumar Kirikasamma ta Jihar.

Jami’in yada labarai na Karamar Hukumar Kirikasamma, Sanusi Soro ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce wutar ta tashi ne a ranar Litinin da misalin karfe 2:00 na dare, inda ta hallaka Malam Muhammad tare da jikkata wasu almajirai biyu.