Daily Trust Aminiya - Gobara: Wike ya ba gwamnatin Sakkwato gudunmawar N500m
Subscribe

Tambuwal tare Wike yayin da kai ziyara Jihar Sakkwato

Gobara: Wike ya ba gwamnatin Sakkwato gudunmawar N500m

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ba gwamnatin Jihar Sakkwato gudunmawar Naira miliyan dari biyar domin sake gina babbar kasuwar Jihar wacce gobara ta cinye a safiyar ranar Talatar da ta gabata.

Wike, ya kai ziyarar kasuwar ranar Laraba, kimanin sa’a 24 da aukuwar gobarar wacce ta yi sanadiyyar asarar dukiyoyi mai tarin yawa.

Mai ba gwamna Tambuwal shawara a kan kafafen yada labarai, Malam Muhammad Bello, ne ya bayyana ziyarar da gwamnan na Ribas ya kai a ranar Laraba.

Gwamna Wike, ya jajanta wa ’yan kasuwar da abun ya shafa, ya kuma ce abin da ya shafi mutanen Sakkwato ya shafi mutanen Jiharsa.

Ya ce gwamnatinsa ta yi alkawarin tabbatar da ganin an gina wa wadanda abun ya shafa shagunansu domin ganin sun dawo kan harkokinsu na kasuwanci.

Tun da farko, gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya zagaya da gwamna Wike wuraren da gobarar ta yi barna, inda ya bayyana masa cewa kasuwar tana da akalla shaguna 16,000 kuma akalla kashi 60 cikin 100 na shagunan gobarar ta shafa.

Tambuwal ya bayyana wa takwaransa na cewa, yayin da gobarar ta kama, jami’an hukumar kwana-kwana na jiha da na tarayya suka kawo dauki don ganin an kashe gobarar.

Baya ga haka, Tambuwal ya jagoranci tawagar gwamna Wike wajen kai ziyarar jaje zuwa fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar a fadarsa da ke birnin Shehu.

More Stories