✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobarar gas ta ritsa da mutane a cikin dare

Motar iskar gas ta kama da wuta a kan hanya a Legas.

Wata motar dakon iskar gas ta yi gobara da dare inda lamarin ya ritsa da akalla mutum 13 a kan hanya.

Mutanen sun samu munanan kuna ne bayar wutar ta tashi a daidai lokacin da motar gas din take wucewa a hanyar zuwa Ikeja, Jihar Legas.

Babban Jami’in Hukumar ba da Agaji ta Kasa (NEMA), Shiyyar Legas, Ibrahim Farinloye, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa, “Mutanen da suka samu raunkan sun samu kulawar gaggawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas, amma an mayar da su Babban Asibin da ke Gbagada.

“Bincike ya nuna akalla ababen hawa 25 kuma sun kone, amma za a ci gaba da tantancewa tare da daukar alkaluma,” inji shi.

Jami’in ya bayyana cewa a cikin mutanen da suka kone din akwai mata hudu da maza tara.

Wutar da ta tashi sakamakon yoyon iskar gas din ta yi ta bindiga, tana yawo a iska a kusa da otal din Sheraton da ke Ikeja.