✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobarar tankar mai: Motoci da dama sun kone a hanyar Legas zuwa Ibadan

Tuni dai jami’an kwana-kwana suka yi wa wajen kawanya domin kasheta.

Ababen hawa da dama ne suka kone kurmus bayan da wata tanka makare da mai ta yi bindiga sannan ta kama da wuta a yankin Ogere da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan a safiyar Talata.

Har yanzu dai babu tabbacin ko an sami asarar rai a hatsarin wanda ya haddasa mummunan cinkoson ababen hawa a hanyar wacce take zama wata mahada tsakanin Jihar Legas da sauran Jihohin Najeriya.

Tuni dai jami’an kwana-kwana da sauran jami’an tsaro suka yi wa wajen kawanya domin kashe wutar.

Kwamandan shiyya na Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) a Jihar Ogun, Ahmed Umar ya ce tuni suka aike da jami’an ceto daga Shagamu da kuma Ogere zuwa wajen.

Ya ce, “Gaskiya wutar ba karama ba ce, kuma ba zamu iya kiyasta adadin motocin da suka kone ba.

“An tuntubi jami’an kwana-kwana na jihar Ogun kuma sun halarci wurin ba tare da bata lokaci ba. Suna kan aiki kuma zasu shawo kanta ba da jimawa ba,” inji shi.

A wani labarin kuma, anshawarci direbobi da ke amfani da hanyar ta wajen tol-get na Ogere, bangaren Kasuwar Kara da ake ginawa a Ibadan da su yi amfani da wasu hanyoyin.

Sashen kula da bin dokokin ababen hawa na jihar ta Ogun (TRACE) ne ya bayar da shawarar a cikin wata sanarwa.

Kakakin sashen, Babatunde Akinbiyi ya ce, “Yayin da ake ci gaba da aikin ceto tare da hadakar jami’an tsaro, muna ba direbobi shawarar su yi amfani da wasu hanyoyin kamar haka.

“Masu zuwa Legas su yi amfani da hanyar Saapade zuwa Ode/Remo zuwa Iperu zuwa Sagamu, wacce zata sake hada su da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

“Bugu da kari, masu zuwa Ibadan kuma su bi ta hanyar Sagamu zuwa Iperu zuwa Ode/Remo zuwa Saapade sanna su koma kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.”