✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobe za a yi ganawar kai tsaye da ’yan takarar Gwamnan Katsina

Kafofin yada labarai da CDD sun dauki nauyin taron  domin ’yan takarar sun bayyana manufofinsu.

Gobe Asabar ce za a yi taron ganawa da ’yan takarar Gwamnan Jihar Katsina.

Rukunin Kamfanonin Media Trust masu buga jaridun Daily Trust da Aminiya da kuma gidan Talabijin na Trust TV da Gidan Rediyon Trust tare da hadin gwiwar Cibiyar Bunkasa Dimokuradiyya (CDD) da gidan rediyon Vision da Farin Wata da kafar labarai ta KatsinaCity News suka dauki nauyin taron  domin ’yan takarar sun bayyana manufofinsu.

Shugaban Kwamitin Shirya taron, Alhaji Ibrahim Daku Sanyin Katsina, ya ce taron zai gudana ne a Dakin Taro na Hukumar Kula da Kananan Hukumomi ta Jihar Katsina a karkashin jagorancin tsohon Wazirin Katsina Farfesa Sani Abubakar Lugga.

Sannan tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna, Alhaji Abba Musa Rimi ne Uban Taro, yayin da Alhaji Kabir Matazu mai gidan rediyon Vision da gidan talabijin na Farin Wata da takwaransa Alhaji Muhammed Kabir Muhammed, Mukaddashin Babban jami’in Gudanawa na Gidan Rediyon Trust za su zamo masu gabatarwa.