Goron Sallah: Muna dab da kawo karshen ’yan ta’adda a Najeriya – Buhari | Aminiya

Goron Sallah: Muna dab da kawo karshen ’yan ta’adda a Najeriya – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
    Muideen Olaniyi da Abubakar Maccido

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce yakin da ake yi da ’yan ta’adda a Najeriya ya kusa zuwa karshe.

Ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa da ya fitar a ranar Lahadi da yake taya al’ummar Musulmin Nijeriya da na duniya ga baki daya murnar bikin Sallah Karama.

Kamar yadda kakakinsa Garba Shehu ya bayyana a cikin wata sanarwa, Buhari ya ce “An kusa kawo karshen dadadden fadan nan da aka yi da yan ta’addan Boko Harama da ’ya’yanta.”

Buhari ya kuma ce bayan gudanar da ibadar azumi, kamata ya yi a ci gaba da samun hadin kai da yin aiki tare a tsakanin hukumonin tsaro, yana mai ba da tabbacin samar wa hukumonin tsaro kudade da sauran kayan aiki domin ganin bayan matsalar tsaron.

Da yake bayyana irin ci gaban da aka samu a bangaren tsaro, ya ce, “A watan da ya gabata, sojojin sama sun yi nasarar kashe shugaban kungiyar ISWAP a wani hari da suka kai ta sama.

“Tun bayan shigowar sabuwar wannan shekarar, dubban mayakan kungiyar ne suka ajiye makamansu inda aka saka su a cikin shirin gyara hali na Gwamnati.

“Haka kuma an samu nasarar kwato wuraren da a baya suke karkashin ikon yan ta’addan, tare da mayar da garuwan ga ’yan gudun hijirar da suka bar muhallansu.

“A yanzu abubuwa sun fara dawowa daidai a arewa maso gabas.

“A yakin da ake da yan ta’adda, an samu nasarar kakkabe ’yan bindigan a bangaren arewa maso yamma da arewa maso tsakiya,” inji Buhari.

Shugaban ya kuma ce gwamnatinsa tana samun rahotanni na musamman a kan yakin da ake yi da masu satar mai ta haramtacciyar hanya a bangaren Kudu maso Kudu, inda aka gano tare da lalata miliyoyin haramtattun matatun man da aka gano a yankin.

Hakazalika sanarwar ta ce Shugaba Buhari ya ba da umurnin kara wa jami’an tsaro 3,500 matsayi tare da samar da kayan aiki, da ma kuma gina wajen ba da horo a hukumar tsaro.