✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Goyon bayan Rasha: Ba za a haska Gasar Firimiyar Ingila ba a China

Tashoshin China sun kaurace wa wasannin domin nuna goyon bayansu ga Rasha

Tashoshin talabijin a kasar China ba za su haska wasannin Gasar Firimiyar Ingila na karashen mako ba, saboda wasannin za su nuna goyon bayan kasar Ukraine kan mamayar da Rasha ta yi mata.

A yayin bude wasannin na wannan mako, ’yan wasa za su sanya nadi mai dauke da launin tutar Ukraine a damatsensu domin nuna goyon bayansu ga Ukraine, a cewar The Gurdian ta kasar Birtaniya.

Amma kamfanonin da ke da lasisin haska wasannin a kasar China, wato iQiyi Sports da Migu sun nuna ba za su haska wasannin ba gaba daya.

Sun yi hakan ne, duk kuwa da cewa yarjejeniyar da suka kulla da Gasar Firimiyar Ingila ta nuna za su haska duk wasannin gasar ne.

Masu kallon tashoshin biyu sun bayyana cewa babu wasannin wannan makon a jerin shirye-shiryen kafafen na wannan mako, lamarin da ya jawo musu suka daga masu son kallon wasannin.

Abin da kamfanonin na China ke yi tamkar raddi ne ga takunkumin da Birtaniya ta sanya wa Rasha da kamfanoninta saboda yakar Ukraine.

Bayan barkewar yakin ne dai Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) da Hukumar Gasar Zakarun Turai suka haramta wa Rasha da kungiyoyinta da ’yan wasanta shiga harkokin kwallon kafa.

Kawancen China da Rasha

Tun bayan barkewar yakin Rasha da Ukraine, China, babbar kawar Rasha, take taka-tsantsan ta fuskar diflomasiyya, sannan ba ta fito ta soki Rashar ba kamar sauran kasashe.

Idan za a iya tunawa a makon da ya gabata ne Shugaban Kasar China, Mista Xi Jinping da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin suka bayyana cewa kawancensu ba ta da iyaka.

Sanarwar tasu a lokacin wata ziyarar da Putin ya kai kasar China wata alama ce ta kara karfafa alakarsu wajen kalubalantar babbar kishiyarsu, Amurka.

Idan za a iya tunawa a 2020 Gasar Firimiyar Ingila ta soke yarjejeniyar haska wasanninta da ta kulla da kamfanin PPTV na kasar China wanda ta ba wa aikin na Dala miliyan 212 a kasar, saboda bullar annobar COVID-19.

Kafin nan a 2019 gidan talabijin na kasar China (CCTV) ya ki haska wasan kungiyar Arsenal da Manchester City, saboda dan wasan Arsenal, Mesut Ozil, ya goyi bayan ’yan kabilar Uighur, wadanda yawancinsu Musulmi ne da ake gallaza wa a yankin Xinjiang na kasar China.