✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Graham Potter ya ci wasan farko a Chelsea

Wannan shi ne wasa na biyu da Potter ya ja ragamar Chelsea.

Sabon kocin Chelsea, Graham Potter ya fara da cin wasa a karon farko da ya ja ragamar kungiyar Stamford Bridge a gasar Firimiyar  Ingila.

Ranar Asabar Chelsea ta yi nasara a kan Crystal Palace da ci 2-1 a Selhurst Park, karawar mako na takwas a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Minti bakwai da fara wasa Palace ta ci kwallo ta hannun Odsonne Edouard, daga baya Pierre-Emerick Aubameyang ya farke tun kan su je hutun rabin lokaci.

Dan wasan tawagar Gabon ya kafa tarihin cin kwallo a wasansa na farko a Arsenal, yanzu kuma a Chelsea.

Daf da za a tashi daga wasan ne Conor Gallagher ya ci wa Chelsea na biyu da ta hada maki ukun da take bukata.

Wannan shi ne wasa na biyu da Potter ya ja ragamar Chelsea, bayan tashi 1-1 da RB Salzburg a  Gasar Zakarun Turai.

Da wannan sakamakon, Chelsea ta hada maki 13, bayan cin wasa hudu da canjaras daya da shan kashi a biyu.

Kungiyar Stamford Bridge za ta buga wasa na gaba a ranar Laraba da AC Milan a Gasar Zakarun Turai.