✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Guardiola ya tsawaita kwantaraginsa da Manchester City

Guardiola zai ci gaba da jan ragamar kungiyar har zuwa 2025.

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya rattaba hannu a kan tsawaita kwantiraginsa da shekara biyu.

A yanzu kocin dan kasar Sfaniya zai ci gaba da jan ragamar kungiyar har zuwa 2025, kamar yadda kungiyar ta sanar a ranar Laraba.

Kocin mai shekara 51, ya jagoranci Manchester City wajen lashe kofin Firimiyar Ingila hudu da kofin kalubale na FA da kuma Carling tun daga lokacin da ya karbi ragamar jagorancin kungiyar a 2016 kawo yanzu.

“Na yi farin cikin aiki da Pep a kungiyar kwallon kafa ta Manchester City,” in ji shugaban kungiyar, Khaldoon Al Mubarak a cikin sanarwar da ya fitar.

“Ya bayar da gudunmawa mai yawa ga nasara da sauya tsarin wannan kungiyar, kuma zai yi kyau idan muka ci gaba da aiki tare.”

Guardiola a halin yanzu shi ne kociya mafi dadewa a jan ragamar kungiyar tun bayan da ya fara aikin horar da ‘yan wasan a shekarar 2008.

“Na ji dadin kasancewa a Manchester City na tsawon wadannan shekaru,” in ji Guardiola.

Guardiola ya jagoranci Barcelona daga 2008 zuwa 2012, sannan ya shafe shekara uku yana horar da Bayern Munich wanda daga nan ya koma Manchester City.

A halin yanzu Manchester City ce ta biyu a teburin gasar Firimiyar Ingila da maki 32 daga wasanni 14 – maki biyar ke nan tsakaninta da Arsenal wadda ke jan teburin gasar.