✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gudun yin sata ne ya sa na shiga sayar da Wiwi – Matashi

Ya bayyana hakan ne lokacin da ’yan sanda suka yi bajekolin shi a Kano

Wani matashi da aka kama yana sana’ar sayar da Tabar Wiwi a Jihar Kano ya ce neman tsira da mutunci da gudun yin sata ne ya sa ya tsunduma sana’ar.

Matashin, mai suna Abdullahi Abdulrahman mai kimanin shekara 20 da haihuwa wanda ke zaune a unguwar Dorayi da ke Jihar ya bayyana hakan ne lokacin da ’yan sanda suka yi bajekolin shi tare da sauran mutanen da ake zargi a hedkwatar rundunar.

Ya ce, “Lokacin da ’yan bijilanti suka kama ni na riga na gama harhada kayana domin in je in sayar, sannan kuma ni Wiwi kawai nake sayarwa.

“Wannan sana’a ce ke hana ni yin sata. Wiwi da kuma sigari kawai nake sha,” inji matashin.

A yayin bajekolin dai, ’yan sanda a Jihar Kano sun ce sun cafke mutum 128 wadanda ake zargin ’yan daba ne dauke da miyagun kwayoyi da kuma kayan sata a Jihar a lokacin bukukuwan salla.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya jagoranci bajekolin a hedkwatar rundunar.

Kiyawa ya ce “Mun kama mutane 120 wadanda ake zargin ’yan daba ne tsakanin biyu zuwa shiga ga watan Mayun 2022, wato lokutan da ake gudanar da Hawan Idi da Hawan Daushe da Hawan Nassarawa da kuma Hawan Fanisau duk a masauratu biyar da ke Jihar.

“Wadanda aka kama din suna dauke ne da makamai da miyagun kwayoyi da kuma kayan sata,” inji Kiyawa.

Kakakin ’yan sandan ya kuma ce sun samu wannan nasara ne tare da taimakon wasu hukumomin tsaro da kuma ’yan sa kai, domin tabbatar da an samu zaman lafiya da gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali.