✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gumi ya caccaki Gwamnati kan barazanar daukar mataki a kan Daily Trust da BBC

Malamin nan na addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya yi Allah wadai da barazanar da Gwamnatin Tarayya ta yi na sanya wa gidan Talabijin na…

Malamin nan na addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya yi Allah wadai da barazanar da Gwamnatin Tarayya ta yi na sanya wa gidan Talabijin na Trust da BBC takunkumi.

A ranar Alhamis da ta gabata ce, Gwamnatin Najeriya ta ce za ta dauki mataki a kan kafar yada labarai ta BBC da kuma Trust TV kan wani bincike na musamman da suka gudanar daban-daban kan ayyukan ‘yan bindiga a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Kasar.

Ministan Labarai da Al’adu, Lai Muhammad, ya yi ikirarin cewa binciken yana kara kambama ayyukan ’yan bindigar da suka shafe shekaru suna kashe mutane a yankin arewacin kasar.

Sai dai a karatun da ya saba gabatarwa duk mako, Sheikh Gumi ya yaba wa kafafen watsa labaran biyu bisa nuna rashin tsoro wajen gudanar da aikinsu na bankado illar da tabarbarewar da harkar tsaro ta yi a Najeriya.

“Abinda ke faruwa a Najeriya musamman a Arewa maso Yammaci kamar yadda muka gani a binciken da ake magana a kai rigima ce ta kabilanci, da kuma kashe-kashe sakamakon gazawar gwamnati na magance rashin adalcin da ake yi wa Fulani a baya.

“Me ake tsammani daga al’ummar da ba ta rike ilimi da muhimmanci ba sai kiwo kawai ta sani?

“To hada wannan da kuma sauran laifuka manya da aka yi musu tun a baya”, in ji shi.

“Maganar da nake muku har yau Fulani da yawa da ba su ji ba ba su gani ba ana kwace musu shanu a hukumance, ina da kwararan shaidu kan hakan.”

Sheikh Gumi ya ce wani sabon abin tsoron shi ne yadda ’yan Boko Haram suka hade da wasu ’yan bindiga Fulani, yayin da su ma ’yan bindigar na hadewa da Boko Haram a akidunsu na addini da kudurori.

A cewarsa, bai kamata Gwamnatin Tarayya ta zargi kafafen watsa labarai da kambama tabarbarewar tsaro ba, bayan ita da kanta gwamnayin ke ba da tukwuicin mukamai ga wadanda ba su da kwarewa, da kuma jami’an tsaron da suka gaza kare hatta babban birnin kasar da kawunansu ba, ballanta kuma a zo kan sauran al’umma.

“Jami’an tsaron da suka gaza kare Shugaban Kasa da kawunansu, amma sai a bar jaki ana dukan taiki don an bayyana wa al’umma gaskiya”

Shehin malamin ya kuma yi kira ga kafafen yada labaran da kar wannan barazana ta sa su yi kasa a guiwa wajen gudanar da ayyukansu na bankado gazawar gwamnati a fannin kare rayuka da dukiyoyin al’umma duk da makudan kudaden da take kashewa.