✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gurneti ya kashe mutane a Katsina

Gurnetin ya fashe a hannun yaran da suka tsince shi a cikin gona a yayin da suke wasa.

’Yan sanda a jihar Katsina sun ce fashewar gurneti ya yi sanadiyyar wa manoma a garin ‘Yammama da ke Karamar Hukumar Malunfashi ta Jihar.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ta gurnetin ya fashe a hannun yaran da suka tsince shi a cikin gona wanda ya fashe a yayin da suke wasa da shi.

Aminiya ta kawo muku rahton cewar wani abu mai kama da bam ya fashe a garin na kafin daga bisani Kakakin Rundunar SP Isa Gambo ya sanar cewa bincikensu ya gano cewa gurneti ne ya fashe.

SP Isa Gambo ya ce, suna ci gaba da binciken yadda aka samu gurnetin da ake zaton ya fado ne daga daya daga cikin jiragen da ke kai wa ‘yan ta’addar da ke kai hare-hare a yankunan Jihar.

Wasu kuma zargin cewar, ko wani tarko ne maharan suka yi wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutanen da suka rasa rayukansu, wasu kuma na asibiti suna karbar magani.

Amma kakakin ya ce rundunar na ci gaba da binciken gaskiyar samuwar gurnetin da ya fashe ya kuma yi wannan ta’asa.