✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Mali ta fice da G5 Sahel

Sojojin da ke mulkin Mali sun fice daga G5 Sahel duk kuwa da matsin da suke fuskanta daga kasashen waje

Gwamnatin sojin kasar Mali ta fice daga kungiyar G5 Sahel bayan kasashen kungiyar sun ki amincewa da shugabancin karba-karba.

Sojojin sun yi bankwana da G5 Sahel ne duk kuwa da matsin lambar da suka fuskanta daga kasashen waje.

Sanarwa da gwamnatin sojojin ta fitar a birnin Bamako, Mali ta janye dakarunta daga cikin sojojin hadin gwiwa na G5 da ta kunshi kasashen biyar bisa zargin ta da zama ’yar amshin shatar kasashen ketare.

Gwamnatin ta Mali ta dauki wannan matakin ne baya dambarwar gudanar da taron kolin shugabannin kasashen G5 Sahel a Mali.

Cukumurdar ta taso ne sakamakon kujerar naki da wata kasar ta hau bisa hujjar cewa Mali na fuskantar rudanin siyasa a cikin gida, furucin da ya harzuka gwamnaitn sojojin kasar.

Tun bayan kwace mulki da sojojin Mali suka yi da kuma kin amincewarsu da sojin hayar Wagner na Rasha, Mali ta shiga zaman doya da manja da wasu kasashe.

Hakan ne ya kai ga Faransa ta janye sojojinta da ke yaki da ta’addanci a Mali, baya ga wasu jerin takunkumai da kasashen kungiyar ECOWAS ta sanya wa gwamnatin sojin.