✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamna Bello ya rufe duk gidajen karuwai a Kogi

Wannan na zuwa ne a matsayin wani mataki na inganta sha’anin tsaro a fadin jihar.

Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi, ya bayar da umarnin rufe gidajen karuwai da rushe duk wasu gine-gine da ake zargin matattara ce na bata-gari a fadin jihar.

Wannan na zuwa ne a matsayin wani mataki na inganta sha’anin tsaro a fadin jihar.

Gwamna Bello ya bayar da umarnin ne yayin wani taro da ya yi da sarakunan gargajiya da daukacin shugabannin kananan hukumomin jihar ranar Talata a Lokoja.

Uamarnin Gwamnan ya shafi har da rushe wasu gine-gine na kama-wuri-zauna a yankunan Lokoja da Osara da Zango da Itobe da Obajana da sauran sassan da ke kai bai wa masu aikata manyan laifuka mafaka a fadin jihar.

Gwamnan ya kuma haramta sanya takunkuman rufe fuska a bainar jama’a da zummar ganin cikakkiyar fuskar kowa domin magance matsalar tsaro.

Bugu da kari, Bello ya bukaci Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar, shugabannin kananan hukumomi, shugabannin kungiyoyi da kuma hukumomin tsaro da su dauki kidaya gami da bayanan daukacin masu sana’ar acaba da tuka Adaidaita Sahu a fadin jihar.

Domin hakar wannan mataki ya cimma ruwa, Gwamnan ya bai wa sarakunan jihar umarnin hada kai da hukumomin tsaro wajen tabbatar da tsaro a masarautunsu da kuma kai rahoton duk wani yanayin da ba su yarda da shi ba.

Kazalika, Gwamnan ya jajanta wa iyalan jami’an tsaron a suka rasa ransu a yankin Karamar Hukumar Ajaokuta ta jihar.