✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Gwamna Buni ya lashe Zaben Gwamnan Yobe

Sakamakon zaben gwamna da Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) reshen Jihar Yobe ta shelanta cewar,  Gwamna Mai Mala Buni na jam’iyyar APC…

Sakamakon zaben gwamna da Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) reshen Jihar Yobe ta shelanta cewar,  Gwamna Mai Mala Buni na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna a jihar Yobe da Rinjayen Kuri’u masu yawan gaske a tsakanin sa da abokan takarar sa. 

Kwamishinan Hukumar ta zabe mai zaman kanta ta kasa  INEC na jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Abdullahi ne ya sanar da hakan a cibiyar tattara sakamakon zaben dake Damaturu, a daren nan na ranar Lahadi 19/04/2023.

Kwamishinan hukumar zaben ya  ce Gwamna Buni na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 317,113, fiye da na abokin takararsa daga jam’iyyar PDP, Hon. Shariff Abdullahi, mai adadin kuri’u 104,259, wanda hakan na nuna gwamna Buni a matsayin wanda ya samu nasara a zaben da aka gudanar a ranar Asabar 18/04/2023.