Daily Trust Aminiya - Gwamna Masari ya bai wa ‘yan bindiga wa’adin kwana biyu
Subscribe

Gwamna Jihar Katsina Aminu Bello Masari

Gwamna Masari ya bai wa ‘yan bindiga wa’adin kwana biyu

Gwamnan Jahar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya bai wa ‘yan bindiga masu aiwatar da satar shanu, satar mutane tare da yin garkuwa da su don karbar kudin fansa da sauran aiyukan ta’addanci wa’adin kwanaki biyu su mika wuya.

Tare da sakin duk mutanan da ke hannun su da sunan garkuwa ko kuma su fuskanci fushin gwamnati.

Gwamna Masari, ya baiyanawa manema labarai hakan ne a yau Talata ta bakin Sakataren gwamnatin Jahar Dokta Mustafa Inuwa, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin tsaro da sasanci na jahar a rahoton sakamakon taron da suka yi da Babban jami’in rundunar sojoji shiyya ta 8 da ke Sakkwato Janar Aminu Bande, da wakillan wadanda aka yi sasanci da su da kuma wadanda har yanzu basu rungumi sasancin ba.

Kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin Jahar Dokta Mustafa, ya ce, wannan shi ne zama na karshe da su wadannan ‘yan bindiga, kuma nan da kwanki biyu su mika wuya ko kuma gwamnati ta nuna masu irin nata karfin.

Shugaban kwamitin sasancin ya ce, za a samarwa wadanda suka rungumi sasancin wuraren zama domin ci gaba da sauran harkokinsu na rayuwar yau da kullum, su kuma wadanda suka bijire zasu dandana kudar su.

More Stories