✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Wike ya sa a zakulo ‘yan awaren Biafra a Ribas

Gwamnan Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya nemi Shugabannin Kananan Hukumomi 23 da sauran al’ummar jihar da su zakulo masa mambobin Kungiyar ‘Yan Awaren Biafra ta…

Gwamnan Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya nemi Shugabannin Kananan Hukumomi 23 da sauran al’ummar jihar da su zakulo masa mambobin Kungiyar ‘Yan Awaren Biafra ta IPOB da ke jihar.

Da ya ke ba da umurni a taron da ya yi da Shugabannin Kananan Hukumomin a gidan gwamnati da ke birnin Fatakwal, Gwamnan ya ce duk wanda ya bar ‘Yan awaren suka kafa tutarsu ko aiwatar da wani taro a jihar to a bakin kujerarsa.

“Akwai wata Kungiyar ‘yan ta’adda da ake kira IPOB, ba ni na kira su ‘Yan ta’adda ba, Kotu ce ta ce Kungiyar ‘Yan ta’adda ce ba ni ba.

“Gwamnatin tarayya ta ce Kungiyar ‘Yan ta’adda ce, saboda haka IPOB ba za su mayar mana da jiha wajen da za su rika kai farmaki ba.

“A matsayinku na shugabanni, idan ku ka bari haka ya faru, kun cuci rayuwar ‘yayanku,” inji shi.

Wike, wanda ya nuna bacin ransa kan yunkurin ‘Yan awaren na kafa tutarsu a garin Oyigbo, ya gargadi shugaban Karamar Hukumar da cewar kar hakan ta kara faruwa.

“Ku je ku gane wa idanunku abubuwan da suka faru a Oyigbo, sun kona kotu, me Kotu ta yi musu? Sun kashe Soja suka kona shi.

“Ku duba ‘Yan sandan da suka kashe su ka kona su, kuma ku ce mu zauna muna kallon su?”.

Wike ya ce jihar Ribas na daga cikin jihohin da ake zaman lafiya a Najeriya, saboda ba su taba samun rikicin kabilanci kamar yadda ake samu a wasu jihohin ba.

“Ba zamu taba nuna kiyayya ga wata kabila ba, muna zaune lafiya da Ibo da Hausawa da mutanen Edo don muna zaman lafiya da duk wani bako a jihar nan.

“Ya zama wajibi ‘yan Najeriya su yaba wa Ribas a matsayin ta na jihar da ba a taba samun rikici tsakanin kabilu ba,” inji gwamnan.

Gwamna Wike, ya ce mutanen Ribas sun dauki Najeriya a matsayin kasa daya kuma al’umma daya, don haka ba za su bar wasu ‘yan ta’adda karkashin Kungiyar IPOB su haddasa rikici a jihar ba.

Ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar jihar da su sa ido sosai, tare da yin kashedi ga ‘Yan awaren cewar su kiyayi Ribas saboda babu wata Kungiya ko mutane da za su goya musu baya in har shi ne gwamnan jihar.

“Ribas yankin Neja Delta ce, kuma za ta ci gaba da zamanta a matsayin Neja Delta,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa duk wani dan Najeriya na da ‘yancin ya zauna a jihar Ribas in har ba zai kawo tashin hankali ba.

“Muna da Ibo da ke gudanar da halastattun harkokin kasuwanci a nan, kuma za su cigaba da gudanar da kasuwancinsu a nan.

“Amma ‘Yan ta’addan da ake kira IPOB ba su isa su gaya mana abin da za mu yi a jihar mu ba don hakan ba zai taba faruwa ba”.

Ya kuma umurci shugabannin al’umma da su shiga cikin kauyuka su zakulo duk wani dan Kungiyar ‘Yan awaren Biafra da suka sani.

Sai dai kuma ya yi kashedin cewar kar wani ya ci zarafin duk wani Ibo da ke yin halastaccen kasuwancinsa a jihar.

“Sai dai akwai bata garin da suke kiran kansu ‘yan awaren Biafra ta IPOB, Gwamnatin Tarayya ta soke Kungiyar, nima na soke Kungiyar a matsayina na gwamna,” inji Wike.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kare martabar jihar ta hanyar hana ‘Yan Kungiyar ta’addan yin tasiri a fadin jihar.

Ya kuma ce Gwamnatinsa za ta taimaka wa ‘Yan banga da ke jihar sai kuma mutanen gari su sa ido

“Ku taimaka wa jami’an tsaro wajen ganin cewar babu wani abu mai kama da Kungiyar ‘Yan awaren IPOB a jihar Ribas.