✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna ya jagoranci cire ciyawa domin bude makarantu 

Gwamnan da kansa ya jagoranci aikin sassaben ciyawa a makarantun jihar

Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya jagoranci ma’aikatan jihar wajen sassabe ciyawa a makarantu gabanin bude su a ranar Litinin.

Yayin jagorantar aikin a kwalejin Mount Carmel, Ilori, gwamnan ya ce ya yi haka ne domin jan ra’ayin mutane su rika kula da kayan gwamnati a yankunansu.
“Sakon a nan shi ne jaddada taimakon kai-da-kai da bayar da gudunmuwa a wuraren gwamnati.
“Idan gwamnati ta gina wa al’umma wani abu, to mutanen wajen su dauka cewa abun nasu ne.
“Na zo nan ne domin in nuna wa mutane cewar babu wanda ya fi karfin shiga aikin gayya.
“Yana kuma da kyau mu rika taimakon kawunanmu — abu ne mai sauki”, inji shi.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Magaji Olawoyin, da Shugaban Kwamitin Kula da Muhalli na jiha, AbdulRazaq Jiddah na daga cikin mahalarta aikin gayyan.
Gwamnan AbdulRazaq ya kuma duba bangaren makarantar da ruwan sama ya lalata a garin na ilori.
Ya kuma bukaci ‘yan jihar da su rika yin aikin taimakon kai-da-kai musamman ganin yadda tattalin arziki a duniya ke cikin mawuyacin hali a yanzu.
Ya ce gwamnati na da dimbin ayyuka a gabanta saboda lalacewar makarantu da dama suka yi a jihar.
Shugaban Makarantar, Mededem Jacinta, da ta shiga makaranta daga baya ta jinjina wa gwamnan kan ziyara ba-zatar da ya kai wa makarantar.