✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Adamawa ya tsallake rijiya da baya

Wata tifa a sukwane ta yi kan motar da Gwamna Fintiri da wasu kwamishinoninsa ke ciki, inda ta murkushe wasu motoci da ke cikin ayarinsa

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya tsallake rijiya da baya bayan wata tifa ta kwace ta mutkushe wasu motoci a ayarinsa.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu da ya ziyarci wurin da hatsarin ya auku cewa, saura kuris tifar ta yi karo da motar ke ciki, amma direbanta ya yi nasarar kawar da ita da kyar.

“Kafin kiftawa da bismillah abin ya faru, Allah Ne kawai Ya kubutar da gwamnan da sauran mutanen da ke cikin bas din; kar ka so ka ga yadda jami’an tsaro ke tsere neman tsira da rayukansu,” in ji shi.

Jim kadan bayan gwamnan da wasu kwamishinoninsa sun hau bas din bayan halartar daurin aure a Masallacin Agha da ke unguwar Dougirei ne tifar ta zo a sukwane ta yi kan ayarin.

Tifar ta yi raga-raga da wasu motocin da ke ayarin gwamnan a tare da yi wasu ’yanda munanan raunuka.

Ganau din ya shaida wa Aminiya cewa irin gududn ta tifar ke yi ya nuna alamar ta kwace wa direbanta ne, lamarin da ta sa masu aiki ba da hannu tserewa domin tsira da ransu.