✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Anambra na son a rage yawan bautar gumaka a jihar

Ya ce bautar gumaka na saurin habaka yanzu fiye da kowane addini a jihar

Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya hori majami’un jihar da su dada jajircewa su yaki bautar gumakan da a yanzu ya ce ta zama ruwan dare a jihar.

Ya yi wannan kiran ne lokacin da yake kaddamar da ginin cocin Life of Faith da ke rukunin gidajen Gwamnatin Tarayya da ke Onitsha a jihar.

Gwamna Soludo ya ce, “Tun bayan zuwan gwamnatinmu, mun ayyana yaki da bata-gari da wuraren tsafe-tsafensu da masu bautar gumaka da wuraren bautar nasu. Za su kawo duk abin da suke so, amma Baibul dinmu yana hannunmuu na dama.

“Anambra jiha ce ta Allah, amm ya zama wajibi mu ci gaba da addu’a don kwato ta daga hannun miyagu da kuma bata-gari.

“Sannu a hankali, bautar gumaka na kokarin zama babban addini a jiharmu, bai kamata mu yi wasa da hakan ba. Hatta Fafaroma yana wa’azi a kan haka, ni ba wa’azi nake yi ba, amma ina aikata abin a zahiri.

“Idan muka zama tsintsiya madaurinki daya, za mu yi nasara, amma muddin muka rarraba, za mu mutu a daidaikunmu,” inji Soludo.

Ya bayyana jihar a matsayin ta Allah, wacce ya ce ya zama wajibi mutanen cikinta su tashi tsaye wajen yaki da bautar gumakan.

Da ya juya bangaren tsaro kuwa, Gwamnan ya ce kalubalen tsaron da ke addabar jihar ba za su tafi rana daya ba, amma dai suna smaun nasara.