Gwamnan Anambra ya ba mijin da aka kashe wa mata da ’ya’ya N500,000 | Aminiya

Gwamnan Anambra ya ba mijin da aka kashe wa mata da ’ya’ya N500,000

Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo
Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo
    Bashir Isah

Magidancin nan, Jibril Ahmed, wanda tsagerun IPOB suka yi wa matarsa da ’ya’yansa hudu kisan gilla, ya samu tallafin Naira dubu 500 daga Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo.

Sai dai magidancin ya ce duk da haka zai bar Anambra ya koma jiharsa ta asali ta Adamawa don ya fara sabuwar rayuwa kasancewar ’yan ta’addar sun yi wa ahalinsa kisan kare dangi.

A cewarsa, “Yanzu haka da nake wannan zancen, ina hanyar Adamawa ne wanda nan ce jihata ta asali, zan koma can in fara sabuwar rayuwa tun da an shafe mini iyalina baki daya.

“Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Charles Soludo, ya ba ni tallafin N500,000 kuma ina godiya ga ’yan uwa da abokaina bisa tallafinsu gare ni tun bayan aukuwar wannan al’amari,”  inji Jibril Ahmed.

Jibril ya kuma ce daukacin ’yan Arewa mazauna yankin sun fice don tsira da ransu, duk sun koma gida, wasunsu kuma na hanyar komawa.

Kisan gillar da aka yi wa matar mai dauke da tsohon ciki tare da ’ya’yanta hudu ya haifar da ce-ce-ku-ce da yin Alla-wadai a fadin kasa.

Tuni Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi Allah-wadai da farauwar lamarin, tare da cewa makazan za su dandana kudarsu nan ba da dadewa ba.