Daily Trust Aminiya - Gwamnan Bauchi ya sallami kwamishinoninsa

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi

Gwamnan Bauchi ya sallami kwamishinoninsa

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya rushe majalisar zartarwar jihar ya kuma sallami wasu daga cikin masu rike da mukaman siyasa.

Mai ba wa gwamnan shawara kan kafafen watsa labarai, Mukhtar Gidado, ya sanar a ranar Laraba cewa sallamar ta fara aiki ne nan take.

Sallamar ta hada da Sakataren Gwamnatin jihar, Shugaban Ma’aikatan Jihar da kwamishinoni kuma an umarce su da su mika ofisoshinsu ga sakatarorinsu.

Da yake musu godiya kan hidimtawar da suka yi wa jihar, Gwamna Mohammed, ya yi wa wadanda ya sallama din fatan alheri.

Sallamar ta kuma ritsa da daruruwan masu mukaman siyasa a gwamnatin jihar.

Karin Labarai