✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan CBN da Hafsan Sojan Kasa sun ki amsa gayyatar Majalisa

Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Attahiru Ibrahim da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele sun yi watsi da goron gayyatar Majalisar Wakilai wacce ta nemi…

Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Attahiru Ibrahim da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele sun yi watsi da goron gayyatar Majalisar Wakilai wacce ta nemi su bayyana a gabanta domin fayyace wasu batutuwa da suka danganci kudin siyan makaman sojoji.

Aminiya ta samu cewa basu amsa goron gayyatar Majalisar ba wacce ta nemi su bayyana gabanta a ranar 12 ga watan Maris.

Majalisar ta kafa wani kwamitin wucin gadi ne don bincikar harkallar siyo makaman sojoji da kuma na sauran hukomomin tsaro a kasar, ta aike da sammacin ga Gwamnan Babban Bankin da kuma Babban Hafsan Soji amma suka yi mata kunnen uwar shegu

Gayyatar na zuwa ne bayan wani dan majalisar daga Jihar Imo, Bede Eke ya gabatar da bukatar hakan yayin zaman majalisar na ranar Litinin ta makon da ya gabata.

Yayin gabatar da kudirin, Honarabul Eke ya ce sammacin ya zama tilas ne biyo bayan kin amsa goron gayyatar da manyan jami’an gwamnatin biyu suka yi.

A cewarsa, ya kamata Majalisar ta fara daukar matakai masu tsauri a kan jami’an gwamnati masu kin amsa goron gayyatar da ta yi musu a duk lokacin da ta bukata.

“Majalisar tana fuskantar matsaloli da Babban Bankin Najeriya kuma ba zai yi wa mu ci gaba da zuba masa idanu ba don da bazarmu yake taka rawa kasancewar sai mun amince da kasafin kudinsa kafin ya gudanar da ayyukansa yadda ya dace.”

“Abun da kawai muke bukata shi ne Babban Bankin ya yi mana bayani dalla-dalla a kan yadda yake fitar da kudin sayo makamai.”

“Idan kuma akwai abun da suke boyewa, ba za mu kyale ba domin a kullum ana kashe mutane saboda haka ba zai yiwu mu rika bata lokaci muna zaman jiran wata hukuma ta gwamnati ba.”

“Ina kira da a aike wa Babban Hafsan Sojin Kasa da kuma Gwamnan Babban Bankin sammaci, don haka ne kadai zai sanya su fahimci mun dauki lamarin da muhimmanci,” inji shi.

Honarabul Eke ya ce sau hudu Majalisar tana gayyatar Babban Hafsan Sojin kasa yayin da ta gayyaci Gwamnan Babban Bankin sau biyar amma babu karo daya da suka amsa goron gayyatar.