✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Filato: Zaben fid-da-gwani a APC ya bar baya da kura

Mutum 18 da suka nemi jam’iyyar APC ta tsayar da su takarar gwamnan Filato sun ce ba su amince da nasarar da Dokta Nentawe Yilwatda…

Mutum 18 da suka nemi jam’iyyar APC ta tsayar da su takarar gwamnan Filato sun ce ba su amince da nasarar da Dokta Nentawe Yilwatda ya yi a zaben fid-da-gwani ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa masu neman takarar sun bayyana rashin amincewar tasu ne a wata sanarwa da suka fitar, mai dauke da sa-hanun Sakataren kungiyarsu, Dokta Danjuma Sarpiya.

Sanarwar ta ce duk tsare-tsaren da aka bi wajen gudanar da zaben tsayar da dan takarar gwamnan sun saba da ka’idojin da jam’iyyar ta APC ta gindaya.

Masu neman takarar sun kuma musanta cewa an gudanar da zaben fitar da dan takarar gwamnan jihar Filato a karkashin jam’iyyar APC ranar 26 ga watan Mayun nan.

Sanarwar ta yi kira da a sake duba yadda aka ce an gudanar da wannan zabe, tun daga mazabu, don ganin an sake tsara ingantaccen shiri, wanda zai bayar da damar samar da daliget-daliget din da za su sake zabo dan takarar da ya cancanta.

“Tuni mun rubuta wa kwamitin da aka kafa wannan bukata da muke da ita don ganin mun ceto jam’iyyar APC a Jihar Filato.

“Muna da hujja a kan cewa babu inda aka zabi daliget din da suka je suka yi wannan zabe, kamar yadda ka’ida ta nuna.

“Abin da suka fada mana shi ne shugabannin kananan hukumomi da masu mukaman siyasa ne suka zabi wadannan daliget-daliget din da suka je suka fitar da wannan dan takara”.

A daren Juma’a ne dai aka bayyana Dokta Danjuma Sarpiya a matsayin wanda daliget-daliget na APC a Jihar Filato suka zaba don ya yi wa jam’iyyar takarar gwamna.