✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Gombe ya nada sabbin Kantomomi a Kananan Hukumomi 11

Gwamnan ya ce nadin nasu ya fara aiki ne nan take

Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya a ranar Talata ya amince da nadin Shugabannin rikon kwarya a Kananan Hukumomi 11 na jihar.

Sanarwar da ke dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ta ce nadin nasu ya fara aiki ne nan take.

Shugabanin Kananan Hukumomin da aka nada din su ne Alhaji Abubakar Usman Barambu na Karamar Hukumar Akko da Garba Umar Garus na  Balanga, sai Margret Bitrus ta Billiri, da Alhaji Jamilu Ahmed Shabewa na Dukku, da Ibrahim Adamu Cheldu na Karamar Hukumar Funakaye.

Sauran sun hada da Aliyu Usman Haruna na Karamar Hukumar Gombe da Faruk Aliyu Umar na Kaltungo da Ibrahim Buba na Kwami da Salisu Shu’aibu Dendele na Nafada sai Yohanna Nahari na Shongom sai Garba Usman na karamar hukumar Yamaltu Deba.