✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Gombe ya rantsar da sabbin Kwamishinoni 3

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya rantsar da sababbin Kwamishino guda uku a Majalisar Zartarwarsa.

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya rantsar da sababbin Kwamishino guda uku biyo bayan garanbawul da ya yi a Majalisar Zartarwarsa ranar daya ga watan Maris na 2021.

Gwamnan dai ya godewa tsofaffin Kwamishinonin da suka bar aiki bisa kokarin da suka yi a lokacin da suka rike kujerun nasu.

Ya kuma jinjinawa Majalisar Dokokin Jihar kan yadda ta tantance Kwamishinonin cikin kankanin lokaci, inda ya sha alwashin ci gaba da aiki kafada da kafada da ita domin gwamnatinsa ta ci gaba don samun ci gaban jihar.

Kazalika, Gwamna Inuwa ya hori sabbin Kwamishinonin da suyi aiki tukuru tare da kiran ma’aikatan gwamnati da su ci gaba da ba su hadin kai don su sami damar gudunar da aikin su yadda ya kamata.

Da yake jawabi a madadin sauran sababbin Kwamishinonin, Abdullahi Idris Kwami godewa gwamnan ya yi bisa wannan nadin da ya yi musu a matsayin tare da yin alkawari cewa za su ba mara da kunya.

Sauran sabbin Kwamishinonin sun hada da Christopher Abdu Buba Mai Sheru wanda aka ba Ma’aikata Ayyuka na Musamman, Abdullahi Idris Kwami, Ma’aikatar Gidaje da Raya Karkara sai Abubakar Aminu Musa wanda zai kasance sabon Kwamishina a Ma’aikatar Matasa da Wasanni.

Kwamishinonin da suka ajiye aiki a baya dai sune Dakta Ahmed Muhammad Gana, Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya da Mela Audu Nunge, Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka na Musamman da kuma Alhassan Ibrahim Kwami na Ma’aikatar Watsa Labarai.