✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa Hakimai da Dagattan Gombe karin albashi

Gwamnan jihar ya musu karin alawus da suke dauka duk wata.

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya kara wa Hakimai da Dagatai a Jihar albashi, da kuma duba yiwuwar gina musu gidaje.

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu na jihar, Ibrahim Dasuki Jalo ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a ranar Juma’a.

  1. Ba a kasarmu aka kama Nnamdi Kanu ba – Kenya
  2. Manoma 2 sun gurfana gaban kotu kan zargin satar wake

Ya ce a lokacin yakin neman zabe na 2019, Gwamnan ya yi alkawarin kara musu albashi da zarar yaci zabe da ginawa wasu  gidaje tare da yiwa wadanda suke da su kwaskwarima.

Kwamishinan ya kara da cewar, “A baya hakimai suna matakin albashi na 6/1, yanzu kuma an mayar da su matakin albashi na 12/1, inda zasu dinga daukar N15,000 a matsayin alawus kowanne wata.

“Su kuma Dagatai suna kan matakin albashi na 3/1, yanzu an mayar da su matakin albashi na 8/1.”

Kazalika, Kwamishinan ya yi kira da su ci gaba da bai wa gwamnati hadin kai da goyon baya wajen ciyar da Jihar gaba.

Da yake jawabin godiya a madadin hakimai da dagatai, Hakimin garin Gombe da kewaye wanda kuma shi ne Yariman Gombe, Alhaji Abdulkadir Abubakar, ya gode wa Gwamnan bisa la’akari da ya yi na halin da suke ciki wajen yi musu karin.

Yariman Gombe, ya kuma ja hankalin Sarakunan da cewa su zama masu biyayya ga gwamnatin jihar, don taimaka mata wajen kawo matsalar tsaro.

A cewar Gwamnan kuma wannan karin ya fara aiki ne tun daga watan Yunin 2021 inda yanzu za a biya su ariyas na watan shidan.