✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Imo ya sallami kwamishinoni 20

Gwamna Uzodinma ya yi babban garambawul a gwamnatinsa.

Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma ya sallami Kwamishinoni 20 daga gwamnatinsa.

Kwamishinoni takwas ne suka rage a kan mukamansu bayan babban garambawul din da gwamnan ya yi a ma’ikatu 28 da ke Jihar, tun bayan hawansa kan mulki a watan Janairun 2020.

Sanarwar sallar ta ce Kwamishinonin da aka bari a kan mukamansu su ne na Ayyuka, Yada Labarai, Lafiya, Harkokin Mata da kuma Bude Ido.

Sauran su ne Kwamishinan Fasha da  kuma Kwamishinan Wasanni da Harkokin Matasa.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da Kwamishinin Yada Labaran Jihar, Declan Emelumba, ya fitar a ranar Laraba.