✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Imo ya sha da kyar a hannun ma’aikata

Ma’aikatan Hukumar Bunkasa Yankunan da ake hako Man fetur a Jihar Imo (ISOPADEC) sun tare Gwamnan Jihar, Hope Uzodimma, suka farfasa masa motoci saboda rashin…

Ma’aikatan Hukumar Bunkasa Yankunan da ake hako Man fetur a Jihar Imo (ISOPADEC) sun tare Gwamnan Jihar, Hope Uzodimma, suka farfasa masa motoci saboda rashin biyan su albashi na wata uku.

Ma’aikatan na dauke da adduna da sauran makamai a lokacin da suka tare gwamnan; Da kyar jami’an tsaron gwamnan suka lallashe su don kada abun ya kai ga ba hamata iska tsakaninsu.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, SP Orlando Ikeokwu, ya yabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce an kama mutum 15 da ake zargi.

Ikeokwu ya ce: “Ranar 17 ga watan Agustan 2020, da misali Karfe 11:30 na safe gungun wasu mutane da suka ce su ma’aikatan ISOPADEC ne sun tare Gwamnan Jihar Imo a kan hanyarsa ta zuwa Obinze domin gudanar da aiki.

“Gungun mutanen da suka yi ikirarin suna bin albashinsu na wata uku sun tare ayarin motocinsa suka harbe su da fistol kirar gida, wanda hakan ya sa aka fasa gilasai da lalata wasu motocin.

Ya kara da cewa, ‘yan sandan sintirin birnin Owerri sun kai samame a inda abun ya faru inda suka kama mutum 15 da fistol kirar gida da adduna 2 da takunkumin fuska na batar da kama da kaca da kwadon kulle kofa.

“Jami’an tsaron da ke tare da gwamnan sun yi matukar kokarin ganin ba su yi fada da su ba don kauce wa zubar da jini”, inji shi

Ya ce an mayar da wadanda aka kama Sashen Binciken Munanan Laifuka domin yin bincike a natse. Ya kuma ba mutane shawarar kar su rika daukar doka a hannunsu.

Jami’in ya gargadi mutanen garin da cewar ‘yan sanda ba za su amince da karya doka ba a jihar.