✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Yobe ya bude sabuwar kasuwar Nguru mai shaguna sama da 500

An sa wa kasuwar sunan malamin addini, Shehu Ngibrima

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bude sabuwar kasuwar zamani da aka gina a garin Nguru da ke Jihar Yobe wacce aka sanya wa sunan Sheikh Muhammad Ngibrima.

Gwamnan ya kaddamar da kasuwar ne tare da takwaransa na Gombe, Muhammed Inuwa Yahaya da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Ibrahim, a ranar Asabar.

Kasuwar zamani ta Sheikh NGibrima Nguru na dauke da shaguna 505 da wasu gine-gine da suka hada da masallaci da katangar da ta kewaye ta da banki da rijiyar burtsatse da kuma magudanar ruwa.

Kazalika, an gina wa sabuwar kasuwar katafaren wurin ajiye ababen hawa da tashar ’yan kwana-kwana da sauransu.

A cewar Gwamna Buni, aikin kasuwa wani bangare ne na zuba jari da gwamnatin Jihar ta yi don bunkasar tattalin arzikin al’ummarta da kuma sake inganta harkokin kasuwanci a yankin.

“Mun gina kasuwar nan ne a matsayin wani bangare na shirin inganta ci gaban tattalin arziki a cikin al’ummomi,” in ji shi.

Ya kuma ce bunkasar tattalin arziki na bukatar yanayi na daidaito wanda kowa ke samun kwanciyar hankali don biyan bukatu.

A nasa jawabin Sanata Ahmed Lawan, ya ce wannan kasuwar ta zamani za ta bunkasa zamantakewa da tattalin arzikin Karamar Hukumar Nguru.

Ya bukaci al’ummar yankin da su mayar da hankali wajen samar da zaman lafiya mai dorewa, ta yadda za a samu ci gaba.

Shugaban Majalisar ta Dattawa, ya kuma bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 ga ’an kasuwan da ke yankin don kara habaka harkokin kasuwancinsu.