✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Zamfara Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kisa Ga ’Yan Ta ’adda

Jami'an tsaro za su fara bi gida-gida domin zakulo ’yan ta'adda a Jihar Zamfara.

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya sanya hannu kan sabuwar dokar hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin satar mutane ko shanu ko shiga kungiyar asiri ko yi wa ’yan ta ’adda leken asiri a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan cewa jami’an tsaro za su fara bi gida-gida domin zakulo ’yan ta’adda a garuruwan jihar.

“Karkashin dokar, duk wanda aka samu da laifin fashi, satar mutane ko ta shanu ko shiga kungiyar asiri, zai fuskanci hukuncin kisa.

“Haka kuma duk wanda ya bai wa wadannan mutane gudummawa ko yaya take, zai fuskancin hukuncin daurin rai-da-rai ko shekara 20 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba”, in ji shi.

Ya sanar da haka ne a wani shiri na musamman da kafafen yada labaran jihar ranar Talata inda y ce kafa sabbonin dokokin ne bayan wani zama na sa’o’i takwas da gwamnan ya yi da majalisar Tsaron jihar.

Sauran dokokin da Matawallen ya bayyana za su fara aiki a jihar nan take sun hada da:

Dokar ta baci kan zirga-zirgar babura a kewayen Gusau daga karfe 9:00 na dare zuwa safiya.

Domin tabbatar da bin sabuwar dokar, gwamnan ya bai wa jami’an tsaro damar harbe duk wanda suka samu da karya dokar nan take, ko kin tsaywa a shingen bincike da ke jihar.

Gargadi ga Otel-otel din jihar da kada su kuskura su bai wa wani daki ba tare da ya gabatar da wata takardar shaidar game da kansa ba.

Saba wa hakan zai janyo rufe hotel din baki daya da kuma tsatstsauran hukunci.

Shirin dai ya biyo bayan taron tattaunawa ta sa’o’i takwas da gwamnan ya yi da majalisar Tsaron jihar.