✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ba ta sayen makamai a wajenmu – Kamfanin sarrafa makamai na Najeriya

Ya ce, hukumomin sun gwammace su tsallaka ketare su sayo

Kamfanin Sarrafa Kayan Tsaro na Najeriya (DICON), ya zargi hukumomin tsaron kasar da rashin sayen kayan aiki daga hannunsa.

Ya ce, hukumomin sun gwammace su tsallaka ketare su sayo bindigogi da albarusai da sauran kayayyakin aikin da suke bukata.

Zargin ya taso ne a lokacin da kamfanin ke kare kasafin kudinsa na 2023 a gaban Majalisar Wakilai.

Wannan ya sa Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai Kan Sha’anin Tsaro gayyatar shugabannin hukumomin tsaron domin jin dalilin da ya sa suka gwammace su yi cefanen kayan aiki daga ketare a maimakon wajen DICON.

Honarabul  Taofeek Ajilesoro na jam’iyyar PDP daga Jihar Osun ne ya gabatar da bukatar gayyato shugabannin hukumomin tsaron don su zo su yi bayani bayan da Darakta-Janar na DICON, Manjo-Janar Hassan Tafida ya bayyana wa kwamitin abin da ke faruwa.

Tafida ya shaida wa kwamitin cewa hakan na faruwa ne saboda babu wata doka da ta hana hukumomin sayen kaya daga ketare ko tilasta musu sayen kayan a wajen DICON.

Kwamitin Majalisar, karkashin jagorancin Honarabul Babajimi Benson, ya ce, ko dai yaya lamarin yake akwai bukatar fara siyan kayan aikin daga gida kafin a soma tunanin tsallakawa ketare.

(NAN)