✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati na duba yiwuwar haramta acaba a Najeriya baki daya

Hakan ya biyo bayan kammala taron Majalisar Tsaro ta Kasa

Gwamnatin Tarayya ta ce ta fara duba yiwuwar haramta sana’ar acaba kwata-kwata a duk fadin Najeriya.

Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan gwamnati, Abubakar Malami ne ya sanar da haka ranar Alhamis, jim kadan da kammala taron Majalisar Tsaro ta Kasa wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ya ce bincike ya nuna cewa ana amfani ’yan acabar wajen aikin hakar ma’adinai, kuma haramcin zai datse hanyoyin da ’yan bindia da ’yan ta’adda ke samun kudaden shiga.

Malami, wanda yake tare da Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Mohammed Dnigyadi da na Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, yayin jawabin ya ce taron majalisar ya mayar da hankali ne kan hanyoyin da za a bi wajen dakile ’yan ta’addan.

Ya ce ya zama wajibi gwamnati ta dauki matakin cikin gaggawa saboda ’yan ta’adda sun canza hanyoyin da aka san su da su na samun kudade zuwa hakar ma’adinai da karbar kudaden fansa.

Da aka tambaye shi ko gwamnati ta duba wahalar da mutane za su shiga idan aka dauki matakin, ya ce za su fifita bukatar kasa fiya da ta daidaikun jama’a.

Shi ma da yake jawabi, Minista Aregbesola, ya ce an yi nisa sosai wajen tattara bayanai kan harin da aka kai kurkukun Kuje, amma ya koka kan yadda aka kasa yin abin da ya dace a kai.

Ya kuma ce tuni aka mika wa Buhari sakamakon binciken na farko-farko, inda ya bayar da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a fitar da cikakken sakamakon da zarar an kammala binciken.

Aregbesola ya ce duk wadanda aka gano yana da hannu a ciki za a hukunta shi.