✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta sa a tura Abba Kyari Amurka ya fuskanci hukunci

Ma'aikatar Shari'a ta ba da izinin tisa keyar Abba Kyari zuwa Amurka ya fuskanci shari'a kan Badakalar Hushpupi ta Dala miliyan 1.1

Gwamnatin Najeriya ta amince a tura DCP Abba Kyari zuwa kasar Amurka domin ya fuskanci hukunci kan zargin sa da hannu a wata badakala ta Dala miliyan 1.1.

Najeriya za ta tura fitaccen dan sandan ne bayan Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, ya ba da umarnin yin hakan ga Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Malami ya tabbatar a hakan ta sanarwar da kakakinsa, Umar Jibrilu Gwandu ya fitar a safiyar Alhamis, inda ya bayyana cewa bayan nazartar bukatar Amurka na mika mata dan sandan, ya gano cewa babu wata siyasa ko cuku-cuku a cikin zargin da ake masa.

A takardar da ya aike wa kotun game da bukatar gwamnatin Amurka na tura Kyari can domin ya fuskanci shari’a, Malami ya ce, lura da abubuwa masu alaka da zargin da ake wa dan sandan, ba a zalunce shi ba idan aka mika shi ga gwamnatin Amurka, kamar yadda ta bukata.

Ya kuma bayyana cewa babu wani zargi da Abba Kyari ke fuskanta a gaban kotu a Najeriya kan batun, don haka za a iya mika shi domin gurfanar da shi a inda ake tuhumar sa.

Fitaccen dan sanda DCP Abba Kyari — wanda a baya-bayan na ya yi kaurin suna bisa zargin aikata manyan laifuka — na fuskantar zargin ne a shari’ar da ake wa Abass Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi tare da wasu mutum hudu a Amurka kan zargin aikata damfara ta daruruwan miliyoyin Dala ta intanet.

Ana zargin Abba Kyari ya bayar da gudunmuwa a damfarar ta Hushpuppi, dan Najeriya da ke zaune a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) kafin dubunsa ta cika.

Laifukan da ake zargin Kyari da aikatawa a karkashin dokokin Amurka dai su ne na taimakawa wajen yin damfara da kuma safarar haramtattun kudade.

A yayin da waccan badakalar da Abba Kyari ya musa ta sa aka dakatar da shi daga aiki domin bincikar sa, a baya-bayan nan kuma shi da ‘abokan cin mushensa’ suka shiga hannu kan badakalar safarar hodar Iblis mai nauyin kilogram 25 da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta kama.